Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Kara Kasafin Kudin Da Ake Warewa Fannin Ilimi Da Kashi 50 – Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a London (Facebook/Femi Adesina)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a London (Facebook/Femi Adesina)

A kasafin kudin bana, Najeriya ta ware naira biliyan 742.5 cikin jumillar kasafin kudin kasar na naira triliyan 11.7, abin da ya yi daidai da kashi 6.3 cikin 100.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin zai kara kasafin kudin da ake warewa fannin ilimin kasar da kashi 50.

Cikin wata mukala da shugaban ya gabatar gabanin taron kolin da ya dukufa wajen cimma burin bunkasa harkar ilimi a duniya, Buhari ya ce gwamnatinsa za ta kara kudaden ne cikin shekara biyu masu zuwa, kamar yadda kakinsa Femi Adesina ya fada cikin wata sanarwa.

“Mun yi alkawarin kara kudaden da muke kashewa fannin ilimi a shekara, zuwa kashi 50 cikin shekara biyu masu zuwa. Sannan muna fatan karawa ya kai har kashi 100 nan da 2025, adadin da ya haura abin da duniya ta gindaya na kashi 20.”

Taron kolin wanda ke samun jagorancin hadin gwiwar Firai ministan Burtaniya Boris Johnson da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, na fatan samar da kofar da shugabannin kasashen duniya za su yi alkawarin tallafawa shirin bunkasa fannin ilimi na duniya da ake kira GPE wanda ya himmatu wajen kyautata sha’anin ilimi a kasashe da yankuna sama da 90 a duniya.

A kasafin kudin bana, Najeriya ta ware naira biliyan 742.5 cikin jumillar kasafin kudin kasar na naira triliyan 11.7, abin da ya yi daidai da kashi 6.3 na adadin kudin da aka warewa ma’aikatar ilimi.

XS
SM
MD
LG