Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Koma Yajin Aikin Gamagari Idan EL-Rufai Ya Ci Gaba Da Yakar Ma’aikata -NLC


Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)

Kungiyar kwadago ta Nariya wato NLC ta bakin shugaban ta, Kwamared Ayuba Wabba, ta ce ida gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya cigaba da yakar ma’aikata ta hanyar sallamarsu ba bisa ka’ida ba za ta koma yajin aikin da ta dakatar a jihar.

Kungiyar ta NLC ta ce a kullum kofarta na bude domin tattauwa tare da neman mafita da magance matsalar korar ma’aikata da gwamnatin jihar kaduna karkashin jagorancin El-Rufai ke yi ba bisa ka’ida ba, inda ta yi gargadin cewa, idan El-Rufai ya ki yarda a nemo mafita mai dorewa, to ’yan kwadago a fadin Najeriya za su tsunduma cikin yajin aikin gama-gari.

NLC KD
NLC KD

A yayin yajin aikin kwanaki biyar da kungiyar NLC ta shirya a jihar Kaduna a makon jiya, gwamna Nasir El-Rufai ya ki zama a daidaita kan sallamar ma’aikatan da ya yi da farko, amma bayan shiga tsakani da masu ruwa da tsaki suka yi, kungiyar NLC ta dakatar da yajin aikin a karshen mason jiya don neman mafita.

Haka kuma, NLC ta ce, idan har gwamnatin jihar Kaduna ta cigaba da yakar ma’aikata, kungiyar ta ba kwamitin gudanarwa na kasa wato NAC iko nan take ya ci gaba da yajin aikin da aka dakatar a jihar, ya kuma kira mambobinta a fadin Najeriya su shiga yarin aikin ba tare da wata sabuwar sanarwa ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron kwamitin zartarwarta na kasa wato NEC a ranar Alhamis.

Sanarwar dai ta samu sa hannun shugaban kungiyar ta NLC na kasa, Ayuba Wabba da mukaddashin sakatarenta Ismail Bello inda ta ce, kwamitin NEC ya amince a bar kofar tattaunawa a bude domin kawo karshen matsalar da rashin da’a da matakin sallamar ma’aikata ba bisa ka’ida ba da gwamnatin jihar Kaduna ta yi ya haifar.

A makon jiya dai, sai da gwamna El-Rufai da ’yan kwadagon suka yi taho-mu-gama biyo bayan korar ma’aikata dubu 4 ba bisa ka’ida ba da gwamnan ya yi, wanda NLC ta ce ya haramta, ta kuma shiga yajin aiki da zanga-zangar lumana lamarin da bai ma gwamnan jihar dadi ba.

NLC PROTEST KD
NLC PROTEST KD

Rahotanni daga jira Kaduna dai sun bayyana koke-koken al’umma kan matakin na kungiyar NLC wanda suka ce ya gurgunta harkoki na kwanaki a jihar, kafin daga bisani gwamnatin tarayya ta sanya baki kungiyar ta janye yajin aikin don a haye teburin sulhu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG