Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Dama da Matasa a Siyasar jamhuriyar Nijar


Shugaban Jamiyar Lumana Afirka Hama Ahmadou.

Hama Amadou Shine Shugaban Jamiyar Lumana Afirka

Jamiyar Lumana Afirka, ta jamhuriyar Nijar, ta zabi Malam Hamma Amadou, a matsayin shugabanta, duk da kasancewarsa, baya kasar.

Mahalarta taron,sun tantance matsayi da akidar uwar Jamiyar, ta Lumana Afirka, tare da sauya kwamitin ta na zartarwa, da samarda wani sabon kwamiti, mai kunshe da matasa.

Garo na biyu kennan jamiyar ta Lumana Afirka, gudanar da taron ta amma wani abun mamaki shine, ana wannan taron ne batare da shugaban Jamiyar, Malam. Hamma Amadou, wanda ke gudun hijira a kasar Turai.

Bayan zaben sabin shuwagabani, jamiyar ta Lumana Afirka, taron na kasa ya tabbatar da Korar wasu kusochin jamiyar, da suka bujirewa uwar jamiyar, inda suka nuna goyon bayan su ga Gwamnatin shugaba Muhammadu Issufu.

Za'a Dama da Matasa a Siyasar Jamhuriyar Nijar - 3'09"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG