Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tarwatsa Zaben Fidda Gwani Na APC a Bauchi da Gombe


APC
APC

'Yan bangar siyasar jihar Bauchi na jam'iyyar APC sun yiwa wuraren zaben fidda gwani a matakin majalisar wakilai,diran mikiya.

Wadanda abun ya shafa sun ce sun hallara zasu soma zabe sai wasu matasa suka dira wurin suna ta yin zage-zage da soma fasa motoci da adduna da yin ashar.

Da abun yayi tsamari kowa ta kansa yayi . Ba'a iya yin zaben ba. Malaman zaben ma da kyar suka sha. Wani dankara ruwa suka dinga zuba masa. Wani kuma an farfasa motarsa.

Malaman zaben sun ce dalilin rashin tsaro ya sa suka dage yin zaben. Walikan 'yan takarar sunce su suna jira su yi zaben. Ko sau dari za'a yi suna nan daram. Dodon da ya kawo hargitsin ba zasu zabeshi ba.

Yayin da APC ta shiga rikici sabili da zaben fidda gwani , PDP kuwa nata ya wakana lami lafiya har ma an fitar da 'yan takara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG