Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Iya Dasa Kan-Dan-Adam Kan Wata Gangar Jiki?


 Valery Spiridonov, mutuminda za'a yanke kansa a dasa kan wata gangar jiki.
Valery Spiridonov, mutuminda za'a yanke kansa a dasa kan wata gangar jiki.

Wasu likitoci suka ce wannan hauka ne kawai, kuma ba zai yi aiki ba.

Gogaggun likitoci suka ce hauka ne batun wai za'a yi tiyatar dasa kan mutum kan wata gangar jiki, suka ce ba zai yi aiki ba, amma wani likita a kasar Italiya, Sergio Canavero, yace yana shirin yin irin wannan tiyata a wajajen karshen shekara mai zuwa.

Tuni har ya sami maras lafiya dan shekaru 31 da haifuwa, Valery Spridonov, daga Rasha, wanda yake fama da ciwon dake ci ko lalata nama da gabobin jikin dan'Adam.

Akwai likitoci da suke goyon bayan shirin na Dr.Canavero, ciki harda Dr. Michael Sarr, wanda tsohon parfessa ne a fanin tiyata,wanda yake tareda daya daga cikin fitattun cibiyoyin kiwon lafiya na Amurka da ake kira Mayo Clinic. Yace tiyatar tana cike da hadari, duk da haka gwaje-gwaje sun nuna cewa, jijiyoyin gadon bayan dan'adam, da aka sake hadawa, suna iya aiki.

Saboda rashin lafiyarsa,Spridonov, baya iya amfani da gabobin jikinsa, kuma awo ya nuna cewa bashi da lokaci mai tsawo da ya rage a duniya.

Lokacin da za'a yi tiyatan, da zai dauki sa'o'i 36, za'a sa kan Spridonov, yayi sanyi kimanin maki 12 na celcius, sannan a yanke kan-nasa cikin sauri, sai a dasa shi ga wata gangar jikin da aka bada gudamawa na wani da ya mutu, amma aka hada gangar jikin da na'urori, da suke ci gaba da sa shi aiki tamkar yana raye.

Likitoci 100, da wasu ma'aikatan kiwon lafiya, cikinsu harda wadanda suke da kwarewa wajen dasa kai da aka ciro daga gangar jikin dabbobi aka dasawa wasu dabbobin.

XS
SM
MD
LG