Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gudanar da Cikakken Bincike Akan Harin Asibitin Aghanistan


Sakataren Harkokin Tsaron Amurka Ashton Carter

Biyo bayan harin da sojojin saman Amurka suka kai kan wani asibiti dake Kunduz kasar Afghanistan Carter ya tabbatar za'a gudanar da cikakken bayani.

Jiya Lahadi Sakataren harkokin tsaron Amurka Ashton Carter ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike akan harin da mayakan saman Amurka suka kai kan wani asibiti a garin Kunduz dake arewacin Afghanistan.

Harin da aka kai ranar Asabar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 da suka hada da likitocin kungiyar Doctors Without Borders wadda take gudanar da aikin jinkai a asibitin.

Yayinda Ashton Carter yake magana a kan hanyarsa ta zuwa Spain jiya Lahadi ya gargadi mutane su yi takatsantsan saboda akwai yawan rudani dangane da lamarin. Carter yace "zamu zakulo gaskiyar". Carter ya kara da cewa ya ba dakarun Amurka umurni su ba wadanda suka samu rauni taimako.

Tun farko kungiyar Doctors Without Borders wadda ta samo asali daga Faransa ta bukaci a gudanar da cikakken bincike saboda harin ya hallaka ma'aikatan asibitin, wato likitocin kungiyar 12 da kuma masu jinya 10.

Mahukuntan Afghanisan sun tabbatar cewa mayakan Taliban kimanin 10 zuwa 15 ne suka boye cikin harabar asibitin. Mukaddashin gwamnan yankin Hamdullah Danishi ya shaidawa jaridar Washington Post tare da cewa "mun jimre harbe harbensu kafin mu mayarda martani"

Amma mai magana da yawn Doctors Without Borders yace basu sami wani labarin da yace ana harbe harbe a harabar asibitin ba. Yace "ko ma menen dalili babu hujjar kai hari kan asibitin dake aiki kuma yana cike da masu jinya".

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG