Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Sallami ‘Yan Boko Haram 468 Masu Fuskantar Shari’a


Wasu 'yan Boko Haram da suke hannun hukumomin Najeriya
Wasu 'yan Boko Haram da suke hannun hukumomin Najeriya

Ofishin ministan shari’ar Najeriya ya sanar da sallamar wasu ‘yan Boko Haram su 468 cikin wadanda ake tuhuma saboda bincike ya nuna basu aikata wani laifi ba, kazalika za’a saki wasu da ba’a sami wata kwakwaran shaida a kansu ba, koda yake ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro zai yi musu horon sake hali

Ofishin ministan shari’ar Najeriya kuma Antoni Janar ya bada sanarwar sakin mutane 468 saboda ba’a samesu da wani laifi ba. Su dai wadannan mutanen za’a mika su ga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Sai dai kawo yanzu kotun ta yankewa mayakan ‘yan Boko Haram 45 hukumcin daurin shekaru bisa ga laifukan da suka aikata. Wasu 116 suna fuskantar karin tuhuma yayinda aka ce babu isasassun shaidu akan wasu 334.

Wani rahoto da babban mai gabatar da kara da sunan gwamnatin Najeriya, Muhammad Umar Yusuf ya gabatar ne ya tabattarda cewa wasu ‘yan Boko Haram da ake tuhuma suna fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya dake Bauchi.

Akwai wasu 28 da za’a maida shari’arsu a manyan kotunan tarayya a Abuja da Minna

Kawo yanzu dai an saurari kararraki 149 a kotuna hudu inda aka yi watsi da shara’oi 34 sanadiyar rashin isassun shedu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:20 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG