Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Jonathan Ba Zai Zama Lawrence Baggbo Ba - inji Kayode


Sugaba Jonathan da Tsohon shugaba Obasanjo

A wasu kalamun tsohon shugaba Obasanjo ya zargi shugaba Jonathan da son yin abun da Lawrence Baggbo yayi a kasar Ivory Coast yayinda ya sha kashi a zabe.

Daraktan kemfen din shugaba Jonathan Femi Fani-Kayode ya mayarwa tshohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo martani bisa ga zargin da yayi cewa Jonathan na neman hanyar yin magudin zabe ko kuma yayi abun da Baggbo yayi a Ivory Coast.

Wai Obasanjo ya san shugaba Jonathan zai lashe zaben shi yasa yake neman dagula lamura. Yace yakamata Obasanjo ya kai karar hukumar zabe da bayyanan da yake gani sune hanyoyin da za'a yi anfani dasu a yi magudi. Yace domin Obasanjo ya kasa mayarda shugaba Jonathan dan amshin shata ko rakumi da akala shi yasa yake son ture Jonathan daga milki. Banda haka yana son kowace gwamnati ta zo ta zama da hannunsa ciki.

Femi Fani-Kayode yace za'a yi zabe a watan gobe kuma a rantsar da Jonathan ko Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

Mataimakin daraktan Yeriman Muri Isa Tafida Mafindi ya cigaba da cewa kalamun daraktansa bai nuna sun zubar da darajar Obasanjo ba ko sun bata masa rai ba. A'a suna gaya masa cewa ya rike girmansa. Ya bar Jonathan ya shiga zabe wanda yace duk wanda yaci zaben za'a bashi. Yace ina ne Obasanjo ya gano cewa za'a hana zabe kuma za'a yi gwamnatin rikon kwarya. Yace irin wannan maganar bai kamata ta fita daga bakin mai daraja ba.

Akan wai karin makonni shidan da aka domin PDP ta samu tayi kulle-kullen yadda zata ci zabe ne kuma idan bata ci ba, ba zata yadda ba, sai Yeriman Muri yace zato ne kuma magana ce irin ta su Obasanjo da abokanen hamayya. Yace babu wanda ake tilastawa yayi abun da bai kamata ba.

Kwamitin kemfen din yace ba zai yi saurin zargin Obasanjo da yiwa PDP zagon kasa ba ko daukan matakan ladaftar dashi. Femi yace Obasanjo tamkar uba yake gareshi da yake matukar mutuntawa.

Kayode ya zargi Obasanjo da neman a kafa gwamnatin soja, ko ta hadin kasa koma ta dimokradiya ce matuka zai iya juyata kamar waina.Ya kara da cewa shi Obasanjo kansa yayi kokarin ta zarce karo na uku a lokacin da yake shugabancin kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG