Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zabe Akeyi ko Nadi a Afirka?


Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Leo Keyen.
Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Leo Keyen.

Yayin da aka tunkari zaben shekara ta 2015 a Najeriya, Sashen Hausa na Muryar Amurka na shirin kawo wa masu sauraron radiyo sabon shiri mai suna Zabe ko Nadi.

Shugaban Sashen Leo Keyen yayi karin bayani akan dalilin kirkiro wannan shiri.

“Abunda yasa muka kirkiro da wannan shiri, saboda mun san cewa zabe shine tubulin gina domokradiyya. Idan babu zabe mai inganci, zabe tsakani da Allah, zabe wanda za’a zabi irin mutanen da ake so, kuma a jefa kuri’a su ci zabe, a tabbatar da su. To anan ne ake samun tangarda a demokradiyyar duk duniya. Kaga yanzu abunda yasa muka kirkiro wannan shiri, domin duba abunda yake faruwa da zabe a nahiyar Afirka baki daya.

Shugaban yayi karin haske akan yadda ake samun nasarar zabe a kasashen yammacin Afirka.

“Zance ne fa na ilimi, a ilimantar da mutane akan zancen zabe, su san muhimmancin zabe, su san cewa zabe ne za’a yi amfani da shi wajen gina demokradiyya. To idan ba’a yi wannan ba, to wasan yara ake”, inji Shugaban.

Za’a fara watsa shirin Zabe ko Nadi ranar Lahadi ta radiyo da karfe 6 na safe, agogon Najeriya da Janhuriyar Nijar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG