Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Vs Jonathan Kashi Na 1


Dan takarar shugabancin kasa Atiku Abubakar, Disamba 11, 2014.

Bisa dukkan alamu, zaben Shugaban Kasa a Najeriya na shekarata 2015 zai samu fafatawar tsohon Shugaban Kasa Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC mai adawa da Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP mai mulki.

A daren jiya ne wakilan Jam’iyyar PDP daga duk fadin Najeriya, a Farfajiyar Eagle Square suka tabbatar da Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar, inda ya kasance dan takara daya tilo wanda ya nemi goyon bayan wakilan.

Ita kuwa Jam’’iyyar APC ta gudanar da nata zaben fidda gwani ne a filin Teslim Balogun dake birnin Ikko, lamarin da aka share dare ana aikin zabe, har Janar Muhammadu Buhari mai ritaya yayi nasara da kuri’u 3,430.

Yanzu hankulan jama’ar Najeriya sun koma kan watan Fabrairun 2015 lokacin da jama’a zasu fita su jefa kuri’ar shugaban kasa da wasu mukaman shuwagabanni.

Batun da yafi daukar hankulan jama’a a haliin yanzu shine tsaro, lamarin da ake zargin Shugaba Goodluck Jonathan da kasa tabbatar da shi a kasar mai albarkatun man fetur.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG