Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: APC Ta Doke PDP a Legas


Dan takarar shugabancin kasa kuma tsohon shugaba Muhammadu Buhari kafin na APC

Sakamakon zaben da aka yi a Legas ya nuna cewa jam'iyyar APC ta doke jam'iyyar PDP

Sakamakon zaben ya nuna jam'iyyar adawa ta APC ta doke jam'iyyar PDP mai mulkin gwamnatin tarayya.

APC ta samu nasara ne da kuri'u dari bakwai da casa'in da biyar da dari hudu da sittin yayinda PDP ta samu kuri'u dubu dari shida da talatin da biyu da dari uku da ashirin da bakwai.

Sanata Tokunbo Afikuyomi na jam'iyyar APC yace zabe yayi kyau duk da cewa akwai matsaloli nan da can da aka fuskanta a mazabu daban daban musamman a birnin Legas.

To saidai jam'iyyar PDP ta bakin Onarebul Wahab yace suna da ja da sakamakon da aka bayar. Yace akwai hadin baki tsakanin hukumar INEC da wata jam'iyya domin a yiwa PDP magudi. Yace da farko dai naurar zabe bata yi aiki ba a wasu mazabu irin su Ikeja. Yace duk wadannan matsaloli ne da yakama a ce an duba.

Yanzu dai an samu sakamamkon jihohin kudu maso yamma guda shida kuma dukansu APC ce ta lashesu.

Ga rahoton Babagida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG