Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: INEC Ta Dage Zaben 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya a Jigawa


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega

Kodayake za'a fara zabe yau amma ba za'a yi na 'yan majalisar wakilan tarayya ba a jihar Jigawa sabili da wasu dalilai.

Zaben shugaban kasa da na majalisar dattawan tarayya da na majalisar wakilan kasar za'a gudanar a duk fadin kasar yau.

Duk da cewa za'a yi wadannan zabukan yau a jihar Jigawa ba za'a yi na 'yan majalisar wakilan tarayya ba sai wani lokacin.

Hukumar zabe ta INEC ta dage zaben ne sabili da rashin cikar kayan aiki da suke da mahimmaci da zaben. An gano cewa a wasu kananan hukumomi kayan zaben 'yan majalisar bai isa wurinsu ba. Dalili ke nan da hukumar zaben ta dage gudanar da zaben . Idan abubuwa sun kankama zata bada wata ranar da za'a yi.

Dangane da ko hukumar zaben zata gudanar da zaben 'yan majalisar kafin na gwamnoni sai jami'in hukumar yace doka zata bi kafin ta sa rana.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG