Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Shirye-shiryen Zabuka Sun Kankama a Filato


Akwatunan zabe

Shirye-shiryen zabuka sun kankama a jihar Filato ina mutane suna wake-waken wasa 'yan takaransu

Magoya bayan jam'iyyu daban daban suna zagaya babban birnin jihar da tutocin jam'iyyunsu.

Masu keke napep da motoci ba'a barsu a baya ba domin sun lika hotunan 'yan takara akan ababen hawan.

Onarebul Daban shugaban APC na reshen jihar yace su ashirye suke su yi zabe. Bisa ga tsari sun samu wakilansu da zasu sa duk mazaban dake jihar. An horas da wakilan akan yadda zasu lura da mazabarsu. Yace sun zauna da iyayen jam'iyyarsu kan yadda zasu tabbatar ba'a yiwa 'yan takararsu zagon kasa ba. Idan hukumar zabe da jami'an tsaro sun yi adalci kuma ba'a ci mutuncin kowa ba, APC tana goyon bayan zaman lafiya. Amma ba zasu amince da rashin yin adalci a wurin zabe ba.

Michael Dachong jami'in PDP shi ma yace a jam'iyyarsu sun riga sun shirya tsaf. Sun wayar da kawunan magoya bayansu. Sun ja kunnuwansu su gujewa rikici.

Hukumar zabe ta kawo kayan aiki kuma za'a soma rabawa zuwa kananan hukumomi.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG