Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: 'Yan Jarida Su Guji Sanya Ra'ayoyinsu Cikin Rahotanninsu


Shugaba Jonathan tare da 'yan jarida suna tattaunawa.
Shugaba Jonathan tare da 'yan jarida suna tattaunawa.

Shugabannin kafofin yada labarai sun gargadi 'yan jarida su gujewa cusa nasu ra'ayoyin cikin rahotanninsu domin su dakile tashin hankali lokaci da kuma bayan zabe

Malam Yusuf Saulawa shugaban gidan radiyon Nagarta na jihar Kaduna yana cikin wadanda suka yi jawabi a taron da kungiyar 'yan jarida reshen Kaduna ta shirya domin wayar da kawunan 'yan jarida game da yadda zasu gudanar da ayyukansu ba tare da tashin hankali ba.

Gudummawar da 'yan jarida zasu bayar shi ne tabbatar da cewa an yi zabe ba tare da tashin hankali ba. Malam Saulawa yace babu abun da ke kara ruruta wutar tashin hankali irin dan jarida ya dauko rahoto kana ya cusa nashi ra'ayin. Idan har za'a gujewa tashin hankali to 'yan jarida su yi karatun ta natsu, su kaujewa sanya nasu ra'ayin. Ko rahoto ya sosawa dan jarida zuciya ko kuma bai mashi dadi ba wajibi ne ya bayar dashi yadda ya samoshi ba tare da kara gishiri ba.

Wurin bada labari a yishi ba tare da kara wani ra'ayi ba. Dan jarida dole ya zama mai kawo zaman lafiya ba mai tayar da hankulan mutane ba. Malam Haruna Muhammad yace duk abun da mutum zai yi ko ma ba dan jarida ba ne yayi shi tsakaninsa da Allah. Ya tabbata gaskiya yake fada ba karya ba.

Alhaji Idris Yusuf Sule shugaban 'yan jarida na jihar Kaduna ya bayyana makasudin taron.Yace nufinsu ne su wayar da kawunansu su kuma ilmantar da juna akan aikinsu na 'yan jarida domin a tabbatar da zaman lafiya, musamman abun da ya jibanci bada rahotanni akan zabuka da siyasa. Sun yi la'akari da irin kashe-kashe da kone-konen da suka faru bayan zaben shekarar 2011. Basa son a maimaita abubuwan da suka faru a waccan shekarar.

Ga cikakken bayani na Isa Lawal Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG