Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Zamu Je Kotun Duniya Idan Ba'a Yi Zabe Ba - inji Matasan Buhari


Dan takarar shugabancin Najeriya Janar Muhammadu Buhari.

Kungiyar matasa masu goyon bayan Janar Buhari sun ce shure-shure bata hana mutuwa.

Kungiyar matasan ta koka kan ganin yadda jam'iyyar PDP take amfani da karfin mulki domin samun biyan bukatunta.

Kungiyar ta yaba kan abunda ta kira bin doka da oda hukumar zabe karkashin Parfessa Attahiru Jega tayi na dage zaben.

Gameda ko kungiyar da sauran magoya bayan Janar Buhari sun fara razana ne kan dage zaben, shugaban kungiyar na kasa Alhaji Adamu Nguru, yace ko kusa, domin a tarihi akwai kasashe da aka dage zabensu, dagewar ta zamewa jam'iyyar hamayya da kasashen alheri.

Daga nan ne yayi barazanar cewa muddin aka kasa gudanar da zabe ranar 28 ga watan Maris kamar yadda aka yi alkawari, to kungiyar zata tafi kotun duniya domin neman a bi musu hakinsu.

Ga rahoto

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG