Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023-KANO: Tarihin Rayuwar Kwankwaso


Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

An haifi Mohammed Rabiu Musa da akafi sani da Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 67 da suka shude a garin Kwankwaso na karamar hukumar Madobi a jihar Kano Najeriya.

Ya halarci karamar makaranntar firamare ta Kwankwaso da babbar firamare a garin Gwarzo. Sai makarantar koyon sana’o’I ta Wudil kana daga bisani ya wuce kwalejin koyon sana’o’I da kere-kere ta Kano wato Technical College Kano, inda bayan kammalawa ya tafi kwalejin fasaha ta Kaduna, inda ya samu karama da babbar Diploma.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala karatun Digiri na biyu akan fasahar injiniyan samar da ruwa a Jami’ar Lougborough dake kasar Burtaniya a shekarar 1985, kana a bara ne ya kammala karatun digiri na uku wato Ph’D a Jami’ar Sharda ta kasar Indiya.

Yayi aiki a kamfanin WRECCA mai aikace-aikacen gina madatsun ruwa da hanyoyin mota mallakar gwamnati Kano tsawon shekaru 17, kana daga bisani ya shiga harkokin siyasa a shekarar 1991, har ma ya zama dan majalisar wakilai ta Najeriya, inda aka zabe shi mataimakin shugaban majalisar.

Bayan rushewar majalisar a shekarar 1993, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya zama wakili a zauren babban taron kasa na sauya fasalin kudin tsarin mulki a shekarar 1995 a zamanin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Hon. Habibu Hassan Elyakub, tsohon dan majalisar dokokin Kano ne kuma sun fito lardi guda da Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kwankwanso tun yana yaro akwai alamun nutsuwa a tare dashi, kuma mutum ne mai son alkinta kudi da abin daya mallaka.

A shekarar 1999 ne aka zabi Dr Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin gwamnan Kano a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP bayan Najeriya ta dawo tafarkin dimokaradiyya, kuma ya ja ragamar gwamnatin Kano tsawon shekaru hudu

Hon. Isyaku Ibrahim Kunya daya kasance cikin hadiman gwamnan da suka yi aiki kud da kud a gidan gwamnati, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso nada hangen nesa a sha’anin shugabanci da tafiyar da harkokin gwamnati, hakan ta sanya inji shi, ya sami damar kirkiro da sabbin abubuwa da zasu ciyar da rayuwar al’umma gaba, musamman a fannin ilimi tun daga tushe.

Gabanin ya zama gwamna, tun yana ma’aikacin gwamnati, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya fara nuna kishin al’umar yankin daya fito, a cewar Hon Habib Hassan Elyakub, “A lokacin ni ina ma’aikatar ilimi shi kuma yana kamfanin WRECCA mallakar gwamnatin Kano, mun kafa kungiyar dalibai da ma’aikatan ‘yan asalin yankin hayin Kogi, zamanin muna karkashin gundumar Rano, saboda da-ma mun lardin mu yana fuskantar kalubalen abababen more rayuwa, hakan ta sanya muka kafa wannan kungiya kuma shine ya shugabance ta, inda muka yi nasarar shige gaba wajen samar da abubuwa a fannin ilimi da lafiya a garuruwan mu da kauyuka”

Masu kula da lamuran mulkin da harkokin dimokaradiyya a Kano sun lura cewa, an sami banbanci da yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya gudanar da gwamnatin sa ta farko da ta biyu a jihar Kano. To amma Hon Isyaku Ibrahim Kunya ya fayyace dalilan hakan. “kila maganar wannan banbanci ba zata rasa nasaba da yadda a lokacin gwamnati ta farko wasu mutane suka rinka kokarin kawowa gwamnati cikas ba, kuma dole ne daya samu gwamnati a karo na biyu ya koyi darasi, domin kada ya maimaita kuskuren daya faru a baya”

A yanzu dai Dr Rabiu Musa Kwankwaso na cikin jerin mutanen dake takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar NNPP a zaben da za a yi watan gobe, kuma Hon. Umar Haruna Doguwa, shugaban reshen jihar Kano na Jam’iyyar ya yi karin haske akan dalilan Kwankwaso na yin wannan takara. “Yana da gogewa a bangarori da yawa, ya yi aikin gwamnati, ya zama gwamna, ya yi minister kuma ya yi dan majalisar dokokin Najeriya a lokuta daban daban, wannan ta sanya ya ke da sanin makama, kuma gashi da kishin Najeriya da mutanen ta don haka muke ganin idan ya zama shugaban kasa zai fitar da Najeriya daga halin da take ciki”.

Daga lokacin daya zama gwamnan Kano a shekarar 1999 zuwa yanzu da ya ke neman ya zama shugaban Najeriya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magoya baya da daliban siyasa da dama, koda yake wasu daga cikin su ba sa tare a yanzu. Alhaji Umar Labaran Danga, mai lakabin Shehin Kwankwasiyya na cikin tsaffin daliban sa na kud da kud a siyasa. “Dr Rabiu Musa Kwankwaso mutum ne mai jajircewa akan abin daya sanya a gaba, zai koya maka siyasa muddin kana tare dashi ba tare da banbanci ba, kuma mutum ne mai kokarin kiyaye karya, inda ya yi alkawari yana kokarin ya cika. Amma raunin sa, shine mutum ne bai fiye karbar shawara ba, yana da son kansa, baya so ya ga wani ya fishi, yana son kowa ya zama a karkashin sa, kowa ya zama yaron sa”.

Dr Rabiu Musa Kwankwaso wanda yanzu haka keda mata daya da ‘yaya, a baya bayan nan ya ziyarci cibiyar Chartham House dake birnin London, inda ya kara nanata manofofi da tsare tsaren da zai aiwatar muddin ya zama shugaban Najeriya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:02 0:00

XS
SM
MD
LG