Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Tarihin Atiku Abubakar Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar PDP


Atiku Abubakar (Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Facebook/Atiku Abubakar)

An haifi Atiku a 1946 a yankin Jada na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma nemi takarar shugabancin Najeriya sau biyar in an hada da zaben nan na 2023 inda ya ci nasarar samun tikiti sau uku.

Tun daga kidayar kuri'ar zaben fidda gwani na babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta PDP don babban zaben 2023 aka fahimci Atiku Abubakar ne zai lashe zaben kamar yadda ya lashe irin wannan zaben a 2019.

Atiku wanda a wani lokacin ake ganin ya kan kafa jam'iyyar ko-ta kwana don kar ya rasa damar tsayawa takara, tun bayan sabanin da ya samu da tsohon shugaba Obasanjo a 2007 ya yi bayani kan jam'iyyar PDM.

"Tun a zamanin Babangida aka kafa jam'iyyar PDM sai dai ba a yi ma ta rijista ba, haka kuma zamanin Abacha da Abdulsalami, daga sunanta ne ma aka samu PDP shi ya sa muke aiki tare," a cewar Atiku.

An haifi Atiku a 1946 a yankin Jada na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma nemi takarar shugabancin Najeriya sau biyar kenan indan aka hada da zaben 2023 inda ya ci nasarar samun tikiti sau uku.

Atiku, wanda tsohon jami'in kwastam ne, ya fara neman tikitin takara a 1993 inda Moshood Abiola ya samu tikitin SDP.

Atiku Abubakar a waje gangamin siyasa
Atiku Abubakar a waje gangamin siyasa

A 2007, a lokacin da ya ke matsayin mataimakin shugaban Najeriya, ya nemi takara a jam'iyyar AC da su Tinubu su ka yi amfani da ita wajen shiga APC.

A 2011 ma Atiku ya gwada nema a PDP inda shugaba a lokacin Goodluck Jonathan ya samu tikitin.

Atiku ya sake nema a APC a 2015 amma shugaba Buhari ya samu tikitin. A 2019 Atiku ya yi takara a PDP ya zo na biyu a yawan kuri'u yayin da shugaba Buhari na APC ya lashe zaben.

A wannan karon kuma Atiku ya sake tsayawa takara a PDP don zaben ranar Asabar.

Gwamna Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)
Gwamna Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)

Jigo a PDP Attahiru Bafarawa, ya ce ko kusa ba za a kwatanta gogewar Atiku da sauran 'yan takara ba, ya na mai buga misali da Bola Tinubu na APC.

“A arewa ba za a kwatanta Bola Tinubu da Waziri ba, a kudu ba za a gwada ba, duk mai kishin Najeriya ya kamata ya zabi Atiku, Allah ya taimake shi ya kawo ma na sauyi.”

Baya ga zargin bakin jini da PDP ta yi a baya har masu hamayya da Atiku ke alakanta shi da almundahana, duk da ba a taba tuhumarsa da wani laifi ba, 'yan APC sun kalubalance shi da ya shiga Amurka in ya isa, kuma Atiku ya shiga Amurkar lamarin da ya kawo karshen batun.

Da zarar dawowar shi gabanin zaben 2019, Atiku ya amsa gayyatar wata muhawarar takarar shugaban kasa inda bangaren shugaba Buhari ba su halarta ba.

Hira ta musamman da Aliyu Mustapha shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi da Atiku Abubakar a Washington, D.C
Hira ta musamman da Aliyu Mustapha shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi da Atiku Abubakar a Washington, D.C

Atiku ya fice daga taron yana mai cewa dama shugaba Buhari ne ya ke so su yi muhawara saboda shi ke kan mulki amma sauran ‘yan takara da suka zo babu amfanin muhawara da su.

Dan tawagar yakin neman zaben PDP Abdul Ningi, ya ce Atiku ne kadai ke da zimmar tunkarar APC a zaben.

Ningi ya wanke Atiku inda ya nuna cewa ba ya nuna bambancin addini, kabila ko yanki, ya kara da cewa “ba ya fassara ka don babbar rigarka.”

Yanzu dai sai a jira a ga yanda zaben na yau Asabar zai kasance, inda a ke ganin shata dagar ta fi karfi tsakanin PDP, APC, NNPP da Labour; wato tsakanin manyan ‘yan takara Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Rabi’u Musa Kawnkwaso, da Peter Obi.

Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya cikin sauti:

2023: Tarihin Dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar (PDP) - 4'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
XS
SM
MD
LG