Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023 -‘Yan Takarar Manyan Jam’iyyu Da Magoya Bayan Su Sun Amsa Tambayar Abubuwan Da A Ke Gani Za Su Kawo Masu Cikas


Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar
Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar

A cigaba da yakin neman zaben sabon shugaban Najeriya a ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da magoya bayan su na bayanan abubuwan da a ke ganin za su haddasa mu su cikas.

Lamuran sun shafi rikicin cikin gida, mulkin karba-karba da kalubalen ‘yan awaren Biyafara.

A fili dai ‘yan takarar na caccakar juna a duk inda su ka samu dama kamar misalin yanda Bola Tinubu na APC a Delta ya yi gugar zana ga Atiku Abubakar na PDP da cewa kar gwamnan Delta wanda shi ne mataimakin sa a takara ya bari jihar sa ta zama na’urar dibar kudin takarar PDP.

Shi kuma Atiku a Lagos ya bukaci jama’a su ‘yanta kan su daga bautar da su da iyali daya su ka yi na tsawon shekaru 23.

Yayin da Rabi’u Kwankwaso na NNPP ke cewa kanwar gazawar APC da PDP duk ja-ce, dan takarar Leba Peter Obi na cewa ya na da logar farfado da tattalin arzikin Najeriya da buga misalin irin tsumulmular sa lokacin ya na gwamna Anambra.

Mataimakin shugaban PDP na arewa Umar Iliya Damagun ya ce batun karba-karba da a ke cewa tamkar zai hana PDP kuri’a a kudu, APC kadai ya shafa.

Jigon APC Farouk Adamu Aliyu ya ce kar ‘yan arewa su bijire a jam’iyyar don rashin samun takara a wannan karo, da nuna cewa zabar Tinubu tamkar rama alheri ne na zabar Buhari a 2015.

Farouk Adamu Aliyu
Farouk Adamu Aliyu

Shi kuma kakakin Leba Yunusa Tanko ya nesanta dan takarar su da mara baya ga ‘yan awaren Biyafara, ya na mai cewa gazawar ‘yan takara a arewa ya sa bukatar gwada kamun ludayin ‘yan kudu maso gabar.

Jigon NNPP Buba Galadima ya ce tamkar jemage da ya zama ya ga kowane dare, hakanan su ka san makamar dukkan ‘yan takarar da jiran ranar zabe don kawo sabon lale.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG