Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Burkina Faso: Batun Tsaro Ne Kan Gaba a Matsalolin 'Yan Kasar


Tabarbarewar harkokin tsaro shine kan gaba a jerin batutuwan da ke damun kasar Burkina Faso, inda masu kada kuri’a zasu nufi rumfunan zabe ranar Lahadi 22 ga watan nan don zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin kasar. 

Tashin hankalin mayaka masu tsananin kishin addinin Islama da rikice-rikicen kabilanci sun addabi kasar da ke yammacin Afrika mai yawan jama’a kusan miliyan 21, sun kuma sa mutane sama da miliyan 1 kaurace wa matsugunnasu kuma akalla ‘yan kasar 1,600 aka kashe tun daga shekarar 2015.

Cikin wadanda suka mutu har da akalla sojojin kasar 14 da aka kashe a lokacin da wasu da ake zaton mayakan ne suka yi wa wani ayarin sojoji kwanton bauna a ranar 11 ga watan nan na Nuwamba a lardin Oudalan da ke arewacin kasar, kusa da iyakar Mali da Nijer, abinda kamfanin dillacin labaran Reuters ya ruwaito ministan yada labaran gwamnatin kasar ya fada kenan.

Cikin ‘yan Burkina faso da suka kaurace wa matsugunnasu, mutane fiye da 400,000 ba zasu iya kada kuri’a ba saboda takardun zabensu sun bace ko kuma basu iya yin rijista ba.

XS
SM
MD
LG