Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Fidda Gwani Na Gwamnoni Na Kara Cazawa Jam’iyyar APC Kai


Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci
Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Gabanin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, masu neman takara a jam’iyyar na ci gaba da mara baya ko fadar abin da su ke son a yi don gudun korafi ko ma tafiya kotu a sakamakon zaben.

Wannan na faruwa ne bayan masu son takarar gwamna da ke son kalubalantar gwamnonin jihohin su, ko kuma ba sa shiri da gwamnonin da za su bar gado don haka su ke fargabar adalcin zaben.

Ga mai son takarar gwamnan jihar Nassarawa, Ahmed Aliyu Wadada, ya ce ba ya shakkar ko wane tsari za a yi amfani da shi a fidda gwanin, matukar za a kaucewa abin da ya kira cusa wakilan bogi.

In za a tuna Muryar Amurka ta kawo labarin cewa, jihar Yobe ta dau matakin daidaitawa da cankar sakataren jam’iyyar Mai Mala Buni ya yi takarar.

Gwamna da ke kammala wa’adin mulkin jihar Ibrahim Gaidam, ya ce duk masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun amince da matsayar, ciki kuwa har da Sanata Bukar Abba da ya janye don baiwa gwamnan fagen zuwa Majalisar Dattawa.

Ko ma dai ba tsadar takardar neman takarar shugaban kasa a APC Naira miliyan 45, dama can jam’iyyar na da ra’ayin shugaba Buhari ne dan takarar ta kuma masu goyon bayan jam’iyyar irin su tsohon dan siyasa Abdulkarim Daiyabu sun kara azzama matsayar.

Rashin lashe zaben gwamnan Osun kai tsaye da APC ta yi, ya zama abin muhawara ga jam’iyyar cewa tasirin zama a kujerar mulki ba lalle ne ya kawo nasara ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG