Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Jihohin Bauchi Da Gombe Yana Gudana Cikin Lumana


Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na cewar zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki a jihohin biyu, yana gudana cikin sauki da kwanciyar hankali kuma ma'aikata hukumar zabe sun isa runfunan zaben kan lokaci har ma suka jira masu kada kuri’a.

An bayyan zaben gwamnoni a jihohin Bauchi da kuma Gombe da cewa ya yi sauki idan aka kwatanta shi da na shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan da ya gabata.

Sai dai zaben kujerar gwamnan da na 'yan majalisun jihohin, takara ce mai zafi a tsakanin manyan jam’iyun APC da kuma PDP.

A jihar Bauchi takara ce tsakanin tsohon ministan tarayya Bala Muhammed Kauran Bauchi, na jam’iyar PDP da kuma Gwamna Muhammed Abdullahi mai son yin tazarce a Jam’iyar APC.

A jihar Gombe kuwa takara ce tsakanin tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya wanda a hali yanzu sanata ne dake takarar kujerar gwamna a tutan jam'iyyar PDP.

Abokin takararsa shine Muhammad Inuwa Yahaya daga jam’iyar APC mai adawa kuma wannan shine karo na uku da yake yin takara, ya kuma ce jam’iyarsa zata yi nasara a zaben na yau.

Domin jin cikakken bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG