Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Yi Kukan Yadda Aka Ci Zarafin Ma’aikatanta a Zaben Shugaban Kasa


Yayin da ya rage kwana daya a gudanar da zaben gwamnoni da na Majalisun jihohi a Najeriya, hukumar zaben kasar ta koka kan yadda akai ta afkawa jami'an ta a zaben shugaban kasa da ya gabata.

Da yake jawabi a taron manema labaru Yau a Abuja, shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce sun damu matuka da yadda ake kai Hari akan akwatunan zabe, rajistar zabe, dakunan Jefa Kuri’a da ma na'urorin tantance masu zabe wadanda yan dabar siyasa suka lalata masu a wancan zaben da ya gabata.

Farfesa Yakubu ya ce babbar damuwar ma itace yadda ake garkuwa da Jami'ansu a tursasa masu fadin sakamakon zabe na karya. Al'amarin da yace ba za su amince dashi ba.

Ya tabbatar da cewa ba zasu bada takardar shaida ga duk wanda aka ce ya lashe zabe ta irin wannan hanya ba.

Shugaban hukumar zaben Najeriya ya bada tabbacin cewa zasu yi aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sandan kasar wajen ‘kara inganta yanayin tsaro a zaben da za ayi gobe na Gwamnoni da na ‘yan Majalisun jihohi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG