Masu kada kuri’a a Delhi, babban birnin India, sun dunguma zuwa rumfunan zabe a yau Asabar, domin jefa kuri’unsu a zaben kananan hukumomi.
Ana kallon wannan zabe, a matsayin wani abu da zai iya auna farin jinin gwamnatin Firai Minista Narendra Modi mai kishin kasa.
Zaben na gudana ne, yayin da hukumomin kasar suka sha alwashi ganin an aiwatar da sabuwar dokar nan ta ba da iznin zama dan kasa.
Wannan zabe har ila yau, shi zai zamanto na farko da za a dora Modi akan mizanin karbuwa ga jama’a ko kuma akasin haka, bayan wannan dokar da majalisa ta amince da ita.
Sabuwar dokar, wacce masu sukar ta suka ce za ta muzgunawa Musulmi, ta haifar da jerin zanga zanga a kasar.
Daga cikin jerin zanga zangar da aka yi, akwai wacce mata ke jagoranta, a wata unguwa da ke birnin na Delhi inda ake wannan zabe na kananan hukumomi.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 09, 2023
Kungiyar ISIS Na Kokarin Farfado Da Karfinta a Duniya