Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Ngozi Okonjo-Iweala: Afurka Ta Samu Mai Share Mata Hawaye


Shugabar WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.
Shugabar WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.

Kasashen Nahiyar Afurka da sauran kasashe marasa karfi sai su sha kuruminsu, ga mai share musu hawayensu.

Nasarar da Dr. Okonjo-Iweala, ta samu na zama shugabar Kungiyar Cinakayya ta Duniya (WTO), ba wai nasara ce kawai tata ba, nasara ce ta Nahiyar Afrika baki daya, duk wani bakin fata zai yi murna da hakan.

Idan aka lura za'a ga cewar, ita ce mace ta farko kuma 'yar Afrika ta farko da ta kaiga wannan mukamin. A tarihi ba'a taba dan Afrika da ya rike wannan matsayin ba. Don haka babbar nasara ce ga Nahiyar.

Haka zalika, za'a iya alakanta wannan nasarar tata, idan aka duba irin rawar da tsohon shugaban Majalisar Dinkin Duniya Dr. Kofi Anan, ya yi wanda ya fito da ga kasar Ghana, duk kuwa da cewar bai rike mukamai kamar yadda ta rike ba, amma matsayin shi ya nuna cewar 'yan Afrika mutane ne jajirtattu, kuma masu riko da gaskiya.

Wannan yana daya daga cikin abubuwan da za'a duba a wannan nasarar ta Dr. Okonjo-Iweala. Ana dai sa ran cewa yanzu da 'yar nahiyar Afrika ke rike da wannan mukamin ta ya hakan zai taimakawa tattalin arzikin Nahiyar?

Malam Yusha'u Aliyu, wani mai sharhi a kan al'ammuran tattalin arziki, yana ganin cewar, hakan zai taimakawa kasashen samun bukasa a harkokin kasuwanci, don kuwa tana da kwarewar da ake bukata wajen sanin hanyoyi da za'a iya bunkasa kasuwancin kasa, idan kuma aka lura da cewar daga nahiyar ta fito, tana da gogewar sanin irin bukatun da ake da su wajen dai-daita al'ammura a nahiyar.

Kasancewar Nahiyar Afrika, na da wakilci a Bankin Duniya, babbar nasara ce, wajen ganin an daina zalintar kasashen nahiyar; kasashen nahiyar na hurdar kasuwanci da duk kasashen duniya, amma sau da yawa ana zalintar kasashen.

Amma wannan lokacin za a samu sauyi, don kuwa Dr. Okonjo-Iweala, wadda ta fito daga yankin zata yi iya bakin kokarin ta don ganin ta kwato ma kasashen hakkokin su ga kasashen da ke zalintar su.

Sai a saurari tattaunawar cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG