Accessibility links

Obama Ya Kada Kuri'arsa Kamin Ranar Zabe.


Barack Obama ne shugaban Amurka na farko da zai kada kuri’arsa kamin a fara zabe.
A yammacin jiya Alhamis Mr. Obama ya kada kuri’arsa a wata mazaba a birnin Chicago, cikin jihar Illinois, a mazabarda yayi rijista. Illinois tana cikin jihohi da suka bada dama ga mutane su jefa kuri’arsu kamin ranar zabe, watau 6 ga watan Nuwamba.
Magajin Garin Chicago Ram Emmanuel Yake Tarbar Shugaba Obama A Chicago Lokacinda Ya Yada Zango Domin Kada Kuri'arsa
Magajin Garin Chicago Ram Emmanuel Yake Tarbar Shugaba Obama A Chicago Lokacinda Ya Yada Zango Domin Kada Kuri'arsa

Shugaban na Amurka ya kira jefa kuri’a kamin ranar zabe da cewa, tsari ne da yake da inganci, wadda ya saukaka damuwar zuwa jefa kuri’a a ranar da aka kebe domin zabe. Sai dai shugaban na Amurka bai bayyana wanda ya jefawa kuri’a ba.

Shugaban na Amurka ya yada zango ne a Chicago tsakan-kanin yakin neman zabe da ya kai Florida, Virginia, da Ohio, jihohi uku da aka lakabawa sunan “mazari” sabo da babu tabbas inda suka karkata, kuma duk dan takara da ya sami goyon bayansu, babu shakka shine zai zama shugaban Amurka.

Shugaba Obama, ya gayawa magoya bayansa a Tampa cikin jihar Florida cewa, shirin da abokin hamayyarsa Mitt Romney ya gabatar, gameda gyara ga tattalin arzikin Amurka, wadanda zasu ci gajiyar shirin sune masu hanu da shuni, maimakon ‘yan tsaka-tsaki. Mr. Obama yace irin wannan tunanin ne ya janyo koma bayan tattalin arziki da ake fama dashi.

Shi kuma Mr. Romney a wunin jiya Alhamis, yayi yakin neman zabe ne a jihar Ohio, inda yayi alkawarin inganta ilmi da samar da ayyukan yi. Ya zargi shugaba Obama cewa ya gaza bayyana ajendarsa idan har aka sake zabensa a lokacin mukabalar da suka yi a baya bayan nan, yace dalili kuwa shine domin shugaban bashi da ajenda.
Sakamakon kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa ahalin yanzu ana kunnen doki.
XS
SM
MD
LG