Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Shugaban Kasar Saliyo Ya Shiga Zagaye Na Biyu


Shugaban Hukumar Zabe, Mohamed Nfa'ali yana bayyana sakamakon zaben
Shugaban Hukumar Zabe, Mohamed Nfa'ali yana bayyana sakamakon zaben

Babu daya daga cikin 'yan takara 16 da ya samu kuri'un lashe zaben shugaban kasar Saliyo saboda haka za'a gudanar da zagaye na biyu cikin makonni biyu masu zuwa kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar

Kasar Saliyo zata gudanar da zaben zagaye na biyu a makwanni biyu nan gaba, bayan da babu dan takara daya cikin su 16 da ya samu kashi 55 cikin dari na kuru’un da zasu kai ga lashe zaben a zagayen farkon.


Shugaban hukumar zaben kasar Mohammed Nfa’ali Conteh, shine ya bada wannan sanarwar a wurin wani taron manema labarai da yammacin jiya Talata, mako guda bayan zaben kasar.


Za a fafata a zagaye na biyu ne tsakanin dan takarar jam’iyyar All Peoples Congress mai mulki APC, Dr. Samura Mathew Willson Kamara da kuma dan takarar jami’iyyar Sierra Leon People’s Party Julius Maada Bio, a cewar shugaban hukumar zaben Mohammed Nfa’ali Conteh yayin da yake ganawa da manema labarai a jiya Talata.


Shugaban kasar mai ci yanzu Ernest Bai Koroma na jami’iyyar APC, zai bar gado ne a cikin wannan shekara, bayan ya kammala wa’adinsa na biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG