Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Za Ta Taimakawa 'Yan Democrat a Zaben Nuwamba - Trump


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi ikirarin cewa Rasha za ta yi kokarin ganin ta taimakawa Jam’iyyar Democrat a zaben ‘yan majalisu da za a yi na tsakiyar wa’adi a watan Nuwamba, lamarin da ya ce zai shafi ‘yan takarar jam’iyyar Republican da yake marawa baya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Rasha na kulle-kullen ganin yadda za ta taimakawa 'yan jami'yyar Democrat su lashe zaben 'yan majalisun Amurka da za a yi a nan gaba.

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a jiya Talata, yana mai cewa “ya damu matuka cewa Rasha za ta jajirce domin ta yi tasiri a zaben."

A ranar 6 ga watan Nuwamba za a gudanar da zaben na tsakiyar wa'adi.

Trump ya kuma yi ikrarin cewa, “bisa la’akkari da cewa babu wani shugaban Amurka da ya taba nuna matsin-lamba ga Rasha kamarsa, kasar ta Rasha za ta goyi bayan ‘yan Democrat, domin babu abin da zai sa su mara mai baya."

Wannan ikrari na sa, da ke cewa Rasha za ta goyi bayan jam’iyyar Democrat a zaben, ya yi hannun-riga da matsayar da hukumomin tattara bayan sirri na Amurka suka dauka, da ya nuna cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben shugaban kasar na 2016.

A zaben, za a yi takarar neman daukacin kujeru 435 na majalisar wakilai da kuma kashi daya cikin uku na kujerun majalisar Dattawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG