Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa A Jumhuriyar Nijer


A woman casts her vote for Niger's presidential election at a polling station in Niamey, March 12, 2011.

Asabar ce, al’ummar Jumhuriyar Nijer wadanda suka cancanci kada kuri’a suka yi dafifi zuwa rumfunan zabe zagaye na biyu domin fidda Gwani a zaben shugaban kasa.

Asabar ce, al’ummar Jumhuriyar Nijer wadanda suka cancanci kada kuri’a suka yi dafifi zuwa rumfunan zabe zagaye na biyu domin fidda Gwani a zaben shugaban kasa. Zaben dake sahun gaban matakan da Gwamnatin mulkin sojin kasar ke dauka domin maida mulkin hannun farar hula.A shekarar da ta gabata ce soja suka hambaras da Gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Tandja Mamadou.

Zaben na ran Asabar, shine zagaye na biyu na shugaban kasar Nijer da ake fafatwa tsakanin shugaban ‘yan hamayya Mahamadou Issofou da kuma tsohon friminista Seini Oumarou. A zagayen farko na zaben shugaban jumhuriyar Nijer da aka gudanar a watan Janairun day a gabata, Mahamadou Issofou ne ke sahun gaba da kashi 36 daga cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, shi kuma Seini Oumarou nada kashi 23 daga cikin dari, masu fashin bakin siyasar Nijer sun ce ga dukkan alamu, Mahmaadou Issofou ne ake ganin zai sami nasarar zaben na yau. Akwai Karin bayani na halin da ake ciki bayan labarun duniya.

XS
SM
MD
LG