Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayyana Sakamkon Zaben Shugaban Kasar Niger


'Yan takarar shugaban kasa masu hamayya da juna Mahamadou Issoufou, a hagu, da Seini Oumarou a dama suna gaisawa

Hukumar zaben jumhuriyar Nijer ta bada sanarwar cewa jagoran ‘yan hamayya Mahamadou Issofou, ya sami nasarar lashe zagaye na biyu na zaben fidda gwani a jumhuriyar Niger.

Shugaban hukumar zaben jumhuriyar Niger Abdourhamane Ghousmane ya bada sanarwar ran litinin cewa Malam Mahamadou Issofou ya kada abokin takararsa kuma tsohon friminista Seini Oumarou a zabe zagaye na biyu da aka gudanar Asabar da ta gabata. Ya sami kasha 58 daga cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, shi kuma abokin takararsa ya sami kasha 42 daga cikin dari. An gudanar da zaben shugaban kasar Niger ne da niyyar maida mulkin kasar hannun farar hula bayan an shekara guda sojana jan ragamar mulki bayan sun hambaras da Gwamnatin Mamadou Tandja. Mahamadou Issoufou, shi ya fara samun nasara a zagayen farkon zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Janairun day a gabata. Akwai ‘yan Niger da suka cancanci kada kuri’ar a zaben da yawansu ya kai miliyan shida da dubu dari bakwai. Jami’an hukumar zaben Niger suka ce kasha 35 zuwa 40 daga cikin dari ne suka fita zuwa rumfunan zaben.

XS
SM
MD
LG