Jiya, wato 26 ga watan nan na Satumba ce zagayowar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don jaddada muhimmancin kawar da makamin nukiliya a duniya. Majalisar ta Dinkin Duniya ta ware ranar ce tun a 1946, bayan da Amurka ta jefa ma kasar Japan makamin na nukiliya a yayin yakin duniya na biyu.
A sakonsa na zagayowar wannan rana a wannan shekarar, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce akwai zabi iri-iri na kawar da makamin nukiliya a duniya y ace abin da ya rage kawai shi ne kasashen duniya masu tasiri su bayar da hadin kai don a cimma wannan burin.
Bukin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Amurka da Koriya Ta Arewa ke karce kasa kan batun mallakar makamin na nukiliya. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa akwai makaman nukiliya kimanin dubu 15 a duniya.
Ga dai wakilinmu Babangida Jibrin da cikakken rahoton:
Facebook Forum