Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakuna Na Cinye Wa Makiyayan Kudancin Kamaru Dabbobi


Wasu mazauna kauyukan kudancin Kamaru na barin kauyukansu zuwa wasu wurare, biyo bayan hare-haren da zakuna ke kaiwa dabbobinsu. Hukumomin Kamaru da masu kula da gandun daji na gargadin al’umma kan ci gaba da barazanar da ake fuskanta daga dabbobin daji.

Ali Sambo mai shekaru 45, shi da matarsa da ‘ya ‘yansa uku sun yi ‘kaura daga kauyensu na Djole ranar Asabar bayan da zaki ya kaiwa dabbobinsu hari, Ya ce cikin makonni biyu zakuna sun kashe musu shanu har 53 a kauyukan Adimbi da Djole da kuma Djinga.

Sambo na daga cikin mutanen da suka yi hijira zuwa kauyen Ntui, mai tazarar kilomita 30 daga Yaounde.

Makiyaya irin Sambo, wadanda zakuna ke kashe musu dabbobi, suna tsoron idan har iyalansu suka ci gaba da zama a kauyukan, zasu iya kasancewa cikin hatsari suma.

Maganar da Sambo ya yi kamar ta sauran makiyaya ce, na cewa ya kamata a kashe Zakunan kamar yadda suke halaka musu dabbobi.

Kizito Ombgwa, makiyayin daji ne da jami’an kula da gandun daji suka kai yankin, ya ce aikinsu na farko shine su tabbatar da cewa mutane basa fuskantar barazana. Amma ya ce kamata ya yi a kama Zakunan a mayar da su inda suka fito.

Donnacien Oum, babban jami’in gwamnati ne a yankin da zakunan suke kai hare-haren, ya ce hukumomi na shirin biyan makiyayan kudaden shanunsu da suka rasa.

Ya ce kamata ya yi al’umma musamman ma makiyaya su yi hakuri. Sashen kare hakkin jama’a na ma’aikatar kula da harkokin cikin gida na shirin biyan dukkan wadanda suka rasa dabbobinsu diyya.

Kungiyoyin kare gandun daji da dabbobi sunce kamar yadda namun dajin ke kaiwa mutane da dabbobinsu hari, haka ma suma mutanen ke kaiwa namun dajin hari, da inda suke.

Kasancewar ‘karin yawan mutane da ake samu wanda ya yi sanadiyar mamaye wasu gandun daji, kamar yadda aka mayar da wasu gandun dajin Kamaru suka koma gonaki da kauyuka, shine ke haddasa matsala tsakanin mutane da dabbobin daji kan abinci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG