Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Zaman Lafiya Da Tsaron Kasa Na Sa a Gaba - Seiyefa


Wata motar tankar jami'an tsaro
Wata motar tankar jami'an tsaro

Tabbatar da zaman lafiya da tsaron Nigeria su ne muhimman abubuwa da mukaddashin shugaban hukumar tsaron farin kaya ko DSS, Matthew Seiyefa ya sa gaba tare da tabbatar da cewa duk wadanda ake tsare dasu ba kan ka'ida ba an yi masu adalci

Mukaddashin babban daraktan hukumar tsaron farin kaya ta DSS Mr. Matthew Seiyefa a taronsa da manema labarai bayan ya kama sabon aikinsa ya jaddada cewa a tsarinsa zaman lafiya da tsaron Nigeria ne farko da zai sa gabansa yanzu.

Ya ce zasu yi iya kokarinsu wajen kare jama'a tare da gudanar da ayyukansu cikin tsarin da dokar kasa ta tanada. Baicin hakan zasu karfafa kokari wajen tattara bayanan sirri tare da tantance su domin tsare Nigeria. A cewarsa suna cikin tsarin dimokradiya ne kuma ayyukansu zasu bi tsarin da ya dace da dimokradiya.

Bugu da kari, daraktan ya yi alkawarin sake duba tsarin da aka bi a baya,inda hukumar ke tsare mutane ba bisa ka'ida ba.

Masana irinsu Dr Kole Shettima, na maraba da matakin da mukaddashin ya ke shirin dauka. Ya ce maganar Mr. Seiyefa ta farantawa mutane rai, saboda an san cewa akwai mutane da ake tsare dasu da ba'a san inda suke ba, wasu ma ba'a san ko suna da rai ba. Ya yi misali da wani dan jarida da aka tsare sai bayan shekaru biyu aka sako shi, bayan da iyalansa suka dauka baya da rai. Ya ce akwai mutane da yawa da aka kama da ba'a san da labarinsu ba. Ya kamata a duba, duk wanda yake da laifi a kaishi kotu. Wanda kuma bashi da laifi a sake shi, a nemi gafararsa kana a biyashi diya.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG