JOS, NIGERIA —
A shirin Zamantakewa na wannan makon mun tattauna ne kan tasirin hukumar kula da harkokin kiwo da dangoginsa, da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jaddada don bunkasa tattalin arzikin kasar a bangaren kiwon dabbobi.
Tun bayan kafa kasar Najeriya 'yan boko suke ta fafutukar a samar wa sashen kiwon dabbobi ma'aikata ta musamman da zai kula da harkokin kiwo, maimakon hadewa da ma'aikatar gona da ta fi ba da fifiko wa bangaren abinci.
Wakilan kungiyar Miyetti Allah a Najeriya sun yaba da samar da hukumar, wanda suka ce za ta tsara yadda makiyaya za su fahimci yadda ake kiwo irin na zamani.
Saurari cikakken shirin da Zainab Babaji ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna