Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zambiya Tace Ba Zata Kama Shugaba Omar a-l Bashir Na Sudan Idan Ya Halarci Taron Koli Da Za'a Yi A Kasar Makon Gobe


Omar al-Bashir (File Photo)

Kakakin gwamnatin Zambiya,yace kasar zata yi amfani da mastsayar Tarayyar Afirka wacce tace a yi watsi da sommacin da kotun kasa da kasa ta bayar,domin babu kotu d a ta sami al-Bashir da laifi.

Gwamnatin Zambia ta bada labarin ba zata kama shugaban Omar al-Bashir na Sudan ba,idan ya halarci taron koli da za’a yi kasar cikin makon gobe.

Wani kakakin gwmnatin kasar, yace Zambia tana mutunta matsaya da Tarayyar Afirka ta cimma, na watsi da sommacin kotun kasa da kasa,mai hukunta manyan laifuffuka,da cin zarafin bil’adama ta bayar kan shugaban na Sudan.

Tarayyar Afirka tace ba’a yankewa shugaban na Sudan wani hukunci ba, saboda haka babu dalilin kama shi.

Shugaban na Sudan bai fito fili ya bayyana ko zai halarci taron na makon gobe ba.

XS
SM
MD
LG