Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuminda kasashen Duniya suka amince shine aka zaba shugaban kasar Ivory Coast , Allasanne Outtara, Ya Fara Daukan Matakan Tilastawa Laurent Gbagbo, Ya Sauka


Shugaban 'yan hamayya na Ivory Coast,Allassane Ouattara da manzon Majalisar Dinkin Duniya zuwa Ivory Coast, Choi Young-Jin.

Mutumen da kasashen duniya suka amince akan shine aka zaba sabon shugaban kasar Ivory Coast, ya fara daukan matakan tilastawa wa shugaban da yaki sauka, Layrent Gbagbo, ya saki ragamar mulki ko bai tashi ba. Daya daga cikin matakan da Alassane Ouattara ya soma dauka shine umurnin day a baiwa Babban Bankin Afrika ta Yamma da cewa ya daina baiwa Mr. Gabgbo kudaden gwamnati.

Mutumen da kasashen duniya suka amince akan shine aka zaba sabon shugaban kasar Ivory Coast, ya fara daukan matakan tilastawa wa shugaban da yaki sauka, Layrent Gbagbo, ya saki ragamar mulki ko bai tashi ba. Daya daga cikin matakan da Alassane Ouattara ya soma dauka shine umurnin day a baiwa Babban Bankin Afrika ta Yamma da cewa ya daina baiwa Mr. Gabgbo kudaden gwamnati. Hedkwatar wannan bankin, wanda kasashen ASfrika takwas ke anfani das hi, tana a Senegal ne. Kuma idan bankin ya bi wannan umurnin na Mr. Ouattara to Mr. Gbagbo zai shiga matsala babba don ba zai iya samun kuddin biyan ma’aikatan gwamanti da sojoji albashinsu ba. Daman dai Hadaddiyar Kungiyar kasashen Afrika ta AU da MDD da sauran cibiyoyin hulda na duniya dun Mr. Ouattara ne suka amince akan shine wanda ya lashe zaben shugaban kasan da aka kamala a cikin watan jiya. Sai dai kuma Mr. Gabgfbo yaki sauka kuma yayi kunnen uwar shegu ga duk kiranye-kiranyen da ake masa na ya saki ragamar mulkin. A jiya ne mutumen das hi Mr. Ouattara ya zaa ya zamar mishi P-minista, Guilaume Soro yace a cikin makon nan shi da magoya bayansa zasu cira, zasu kwace ma’aikatun gwamanti. Yace jibi ran Alhamis zasu je su kwace tashar TV ta kasar, kuma ya shiga opishin da aka tanada na frayim-minista. Koda yajke izuwa yanzu ba’aji wani murtani daga bangaren Mr. Gabgbo ba, an san cewa a jiya din sojan dake biyayya gas hi Mr. Gabgbo din sun toshe hanyoyin dake zuwa otel din da Mr. Ouattara yake zaune a ciki.

XS
SM
MD
LG