Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga Tana Bazuwa A Kasashen Musulmi


'Yan zanga-zanga su na kaucewa daga barkonon tsohuwar da 'yan sanda suka jefa musu a al-Qahira ta Misra.

A yayin da ake kara nuna fusata kan wani faifan bidiyo na nuna kin jinin addinin Islama da yin batunci ga Annabi Muhammad (saw)

An barke da sabbin zanga-zanga yau jumma'a a fadin kasashen Musulmi, inda ake kara nuna fusata kan wani faifan bidiyo na nuna kin jinin addinin Musulunci wanda aka sanya a Intanet.

Zanga-zanga ta baya-bayan nan ta barke a Tunis, babban birnin kasar Tunisiya, inda 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa kan 'yan zanga-zanga dake jifa da duwatsu. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun samu nasarar tsallaka katangar da ta kewaye ofishin jakadancin.

Har ila yau, wannan fitina ta yadu zuwa kasar Sudan, inda shaidu suka ce 'yan sanda sun yi arangama da dubban 'yan zanga-zanga da suka doshi ofishin jakadancin Amurka a Khartoum. An bayar da rahoton cewa 'yan zanga-zanga sun samu sukunin shiga cikin harabar ofishin jakadancin kasar Jamus.

Jumma'a ce rana ta hudu da fara yin zanga-zanga a kan wannan fim, wanda ya zamo batun da aka yi ta magana a kai a lokacin sallar Jumma'a a fadin Gabas ta Tsakiya, da yankunan kudanci da gabashin Asiya da kuma nahiyar Afirka. Da yawa daga cikin 'yan zanga-zangar su na kai farmaki ne a kan kasashen da suke gani ba su dauki kwararan matakan hana yin wannan fauifan bidiyo ba.

Ofisoshin jakadancin Amurka da na kasashen ketare sun kara irin matakan tsaron da suke dauka a bayan da aka fara yin wannan zanga-zanga ranar talata.

Wuraren da aka gudanar da zanga-zanga mafiya girma sun hada da birnin al-Qahira a Masar, inda a yau jumma'a 'yan zanga-zanga suka yi arangama da 'yan sanda dake harba barkonon tsohuwa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG