A yau Lahadi, ‘Yan sandan Hong Kong, sun yi amfani da kulki da abin feshi mai sa kwalla, wajen tarwatsa masu zanga zanga a wani gari da ke kusa da kan iyakar yankin da kasar China.
Dubun dubatar masu boren ne suka yi dandazo a garin wanda ake kira Sha Tin domin yin zanga zangar.
Wannan zanga zanga wacce ake yi a kowanne mako, ta samo asali ne tun daga wani bore da ya kunno kai, bayan da hukumomin yankin na Hong Kong suka yi yunkurin samar da wata doka da za ta sa a rika tura wadanda ake tuhuma da laifi zuwa kasar ta Sin domin a yi musu shari’a.
Ko da yake, hukumomi sun janye wannan kudurin doka, amma yanzu masu zanga zangar sun mayar da hankulansu ne kan yadda China ke kokarin ganin ta cusa kanta wajen gudanar da harkokin mulkin yankin.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 26, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe