Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga Zangar Kin Jinin Dokar Zama Dan Kasa A India Ta Rikide Zuwa Tashin Hankali


Zanga-zangar kin jinin dokar zama dan kasa a India ta rikide zuwa tashin hankali a ranar Lahadi, sa’adda ‘yan sanda suka shiga ginin wata jami’a suka harba barkonon tsohuwar ga daliban da ke zanga-zangar.

Daliban jami’ar Islama ta Millia, sun ce ‘yan sanda sun harba musu hayaki mai sa hawaye a cikin dakin karatu, kana kuma suka doki wasu dalibai da sanduna, kafin su toshe dukkan kafofin shiga jami’ar.

Akalla dalibai dozin biyu ne ke karbar kulawa da magani a asibitin Delhi.

Shugabannin dalibai sun zargi wadansu daga waje da tada tarzoma, inda suka ce a wata sanarwa, sun shirya zanga-zangar lumana ne kawai ba tashin hankali ba.

Sai dai da sanyin safiya kuma an kona motocin safa uku. ‘Yan sanda sun ce an kuma raunata jami’an su shida a yamutsin.

Akalla tashoshin jiragen kasa 15 ne aka rufe a ranar Lahadi sakamakon tarzomar.

Masu rajin kare hakkin bil’adama sun yi kira a shafin sadarwa na Twitter, da a yi zanga-zanga a wajen ofishin ‘yan sanda, inda suke bada sanarwar yadda za’a yi tafiya a hadu a wajen, duk da yake an rurrufe tashoshin sufurin.

An ruwaito cewa kusan masu zanga-zanga dubu daya suka fantsama akan tituna a ranar Lahadi da ta gabata.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG