Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar Neman Kawo Karshen SARS Ta Canza Salo a Jos


Zanga zangar ENDSARS.
Zanga zangar ENDSARS.

Matasa a birnin Jos da ke jihar Filato sun ci gaba da yin zanga-zanga sun kuma bukaci a yi garambawul don kyautata rayuwar al'ummar Najeriya.

Yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen hukumar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da ‘yan fashi da makami a Najeriya wadda aka fi sani da SARS, yanzu kuma zanga-zangar ta rikide ta koma ta neman yin garanbawul akan yadda jami’an ‘yan sanda ke gudanar da ayyukan su, dama sake fasalin harkokin mulki a Najeriya.

Al’ummar kasar na ci gaba da bayyana mabambantan ra’ayoyi akan zanga-zangar. Wani matashi mai suna Twamsen Danan, daya daga cikin masu zanga-zangar a birnin Jos, ya ce ban da batun kauda rundunar SARS, suna bukatar gwamnati ta duba matsalolin da kasar ke ciki don kawo gyara mai dorewa.

Matasa masu neman rushe rundunar SARS
Matasa masu neman rushe rundunar SARS

Ya kara da cewa, ai matasa suke zaben shugabanni, don haka ya kamata a ce matasan na cin gajiyar dimokaradiyya, ba kawai a yi amfani da su wajen zabe ba amma bayan haka sai a maida su karnukan farauta kawai.

“Babu dalilin da zai sa mu ci gaba da bauta wa ‘yan siyasa, don haka muna bukatar a kawo karshen wannan mulkin na danniya” a cewar Danan.

A hannu daya kuwa Daraktan ilimi na kungiyar JIBWIS a jihar Filato, Alhaji Abubakar Imam Gana, ya na ganin fitowar matasa zanga-zangar; sam ba shi da wani fa’ida.

Ya ce ai akwai matasa masu ilimi, don haka sai su rubuta sakon korafe-korafen su zuwa ga mahukunta, don daukar matakan da suka dace, amma wannan matakin da suka dauka, zai kara durkusar da tattalin arziki ne bayan illar da annobar coronavirus ta yi ga kasar.

Shi kuwa Rabaran Solomon Guruza, na majami’ar ECWA a cibiyar koyon Tauhidi ta Jos, gani ya ke matasa sun fara gane ‘yancin kansu. Don kuwa daga fara zanga-zangar ga shi har gwamnati ta dauki matakin rushe rundunar, ashe kuwa idan jama’a zasu ci gaba da daukar irin wannan matakin a bangarori dabam-daban, kamar Ilimi, lafiya to babu shakka za a iya samun mafita.

Zanga Zangar kin jinin SARS a Jos
Zanga Zangar kin jinin SARS a Jos

Babban abun takaici a yau shine, makarantu na yajin aiki, akan rashin biyan albashin malamai, amma ana biyan ‘yan majalisu kudaden da wasu ke ganin sun yi yawa. Rabaran Guruza ya kuma ce yau gashi jama’a sun ajiye bambance-bambancesu na kabilanci, bangaranci da addini a wannanan fafutukar.

Amma Kwamred Bukhari Nata’ala, mai sharhi kan lamuran yau da kullum, ya duba lamarin ne ta fuskoki biyu inda ya ke cewa zanga-zangar na da alfanu, kuma ta na da rashin alfanu.

“Da ‘yan siyasa na da tausayin talaka wajen samar da abubuwan more rayuwa, to da yanzu ba a kai ga wannan yanayi da ake ciki ba. A ganinsa tun da har gwamnati ta fara sauraron talakawa, to ya kamata a kawo karshen wannan zanga-zangar.

Don karin bayani cikin sauti, sai a saurari rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00



  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG