Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar 'Yancin Turawa Zalla A Nan Amurka Ba Ta Yi Tasiri Ba


'Yan sanda sun shiga tsakanin bangarorin biyu

Masu zanga zangar adawa da nuna bambancin launin fata sun fi masu zanga zangar ganin Amurka ta kasance kasar turawa zalla, lamarin da ya sa zanga zangarsu ba ta yi tasiri ba kamar yadda suka yi zato

Masu zanga zangar kin jinin nuna bambamci sun fi masu zanga zangar ganin kasar turawa zalla da suka yi gangamin daura da fadar shugaban Amurka ta White House jiya Lahadi a yayinda ‘yan sanda suka raba tsakanin su.

‘Yan sanda sun kebe wurin da babu wanda zai shiga a dandalin Lafayette a nan birnin Washington DC, domin hana aukuwar maimatawar abinda ya faru wajen zanga zangar da yan ra’ayin Nazi suka yi a bara a garin Charlottesville jihar Virgina data buge ta zama tarzoma. An zargi wani da yace shi mai ra’ayin Nazi ne da laifin bi ta kan wata mai zanga zanga Heather Heyer yar shekara talatin da biyu da haihuwa da mota ya kashe ta.

Yawancin fushin masu zanga zanga na jiya Lahadi sun baiyana ne cikin kururutawa da suka auna kan kalilan na ‘yan wariyar da suka fito, gangamin da wadanda suka shirya suka kira, gangamin kwato ‘yancin jar fata ko kuma turawa zalla.

Yawancin turawan da suka halarci ganganin sun boye fuskokinsu a bayan tutoci da kellayen da suka daura a fuskosinsu. Sun ki suyi magana da ‘yan jarida.

Ahalinda ake ciki kuma, lauyan shugaban Amurka Donald Trump Rudi Guliani, ya fada jiya lahadi cewa, gungun lauyoyi da suke kare shugaban kasar ba zasu kyale bincike na musmaman kan shishshigin da Rasha tayi a zaben Amurka ya yiwa Mr. Trump tambayoyi kan dalilan da suka sa ya kori tsohon darektan hukumar FBI James Comey.

Juliani yace tambayar gadan zare ne mai binciken yake shiryawa Mr. Trump.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG