Shugaban yaa fada a cikin sakon Twitter da ya aike a filin wasan golf a jihar New Jersey, yana mai cewar yakamata mu hada kai a matsayin mu na al’umma daya. Yace yana Allah wadai ga duk wani nau’I na wariyar launin fata da kuma tada zaune tsaye.
Trump ya kara da cewa ya yi tsayin daka wurin kyautata rayuwar marasa rinjayi a kasar kana ya lashi takobin ci gaba da inganta rayuwar Amurkawa baki dayansu.
Kalaman na shugaban martani ne ga wani taron da aka gudanar a bara a Charlottesville a jiahr Virginia, wanda ya sha tsananin suka akai, a lokacin da ya fada cewa akwai mutanen kirki a duk bangarorin maimakon ya yi tir da abin da ya faru.
Magajiyar garin Washington Mauriel Bowser ta fada a ranar Alhamis cewa ta bada umarnin tabbatar da matakan kai agajin gaggawa kafin taron gangamin na yau Lahadi a gandun shakatawa na Lafayette Square dake daura da fadar White House. An kuma bada izinin gudanar da zanga zanga ga masu adawa da wannan taron wanda su kuma zasu yi nasu taro a nan gandun shakatawa, da wasu wurare dake kusa da gwurin.
Facebook Forum