Dan takarar shugaban kasa na Najeriya karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya fitar da jerin sunayen mutane 28 da su ke mu’amala da Shugaba Muhammadu Buhari, alhalin ana zarginsu da tafka almundahana.
Sunayen sun fito ne daga mai bai wa Atikun shawara kan harkar sadarwa, Phrank Shu’aibu. Sunayen sun hada da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimohle da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.
A cikin jerin sunayen akwai wasu gwamnoni da ‘yan Majalisar Dattawa, da kuma daraktan yakin neman zaben shugaba Buhari, Rotimi Amaechi.
Atiku, a zargin na sa, ya tabo batun kudin da aka rubuta an yi badakalarsu da su ka kai biliyoyin Naira, sannan ya kuma bukaci hukumar zaben kasar da ta soke jam’iyyar APC, saboda wai ta zama tungar barayi.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 20, 2023
Gwamnonin Gombe, Bauchi Sun Samu Wa'adi Na Biyu
-
Maris 19, 2023
Seyi Makinde Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo
-
Maris 19, 2023
Yadda Aka Yi Zaben Gwamna A Bauchi
Facebook Forum