Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN VOA: Batun Yadda Tinubu Ya Nada Mata 9 Cikin Ministocinsa - Satumba 10, 2023


Medina Dauda
Medina Dauda

Tun lokacin da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ba mata mukaman Minista 13, wannan shi ne karo na biyu da wani Shugaban kasa zai ba mata mukamai da dama.

Tinubu ya ba mata 9 mukamin Minista wanda ya zama kashi 18 cikin 100. Duk da cewa bai kai abinda mata suke ta fafatukar samu ba tun shekara 1993 da suka yi taron Beijing a kasar China, mata sun ce a dukanin mukamai suna bukatar kashi 35 cikin 100.

A wannan shiri na ZAUREN VOA mata biyu, Madam Ene Ede ta Kungiyar gwagwarmayar kwato wa mata yanci mai suna EQUITY ADVOCATE da Hajiya Bilkisu Ibrahim ta Jamiyyar APC mai Mulki, sai kuma daya cikin masu magana da yawun Kungiyar Kamfe din Shugaba Tinubu Ali M. Ali, za su tattauna kan wannan batun, yaya mata a Najeriya suka dauki wannan yunkuri na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu?

A yi sauraro lafiya:

ZAUREN VOA
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:14:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG