A kalamansa na baina jama'a na farko tun bayan da Trump ya dakatar da tallafin sojan Amurka ga Ukraine, Zelensky ya nemi tsagaita wuta ta sama data ruwa a matsayin matakin farko na kawo karshen yakin shekaru 3 tare da yin alkawarin rattaba hannu akan yarjejeniyar hakar ma'adinai tsakaninsa da Washington.
Rushewar alakar Kyiv da Washington ta lokacin yaki ta bayyana a zahiri tun bayan arangamar cacar bakin data afku a ofishin shugaban Amurka tsakanin Zelensky da Trump a makon daya gabata, abinda ya janyo babbar kawar Ukraine dakatar da tallafin soja mai matukar mahimmanci.
"Ni da tawagata na cikin shirin yin aiki a karkashin jagorancin Shugaba Trump domin samun lafiya mai dorewa," kamar yadda Zelensky ya shafinsa Na X.
"Ganawarmu a Washington, a fadar White House a Juma'ar data gabata, bata gudana yadda ya dace ba," a cewar shugaban Ukraine. "lokaci yayi da zamu gyara al'amura su tafi daidai."
Dandalin Mu Tattauna