A yau laraba da aka shirya za'a fara shari'ar, amma lauyar Theo Bronkhorst, ya nemi kotu ta bashi karin lokaci domin ya shirya , daga nan kotun ta dage fara jin karar zuwa 28 ga watan gobe satumba.
Maharbi Bronkhorst, shine jagoran Walter Palmer, likitan hakori dan Amurka daga jihar Minnestota wanda ya harbe ya kashe zakin da ake kira Cecil, a lamari da nmahukuntan kasar sua kira d a cewa ya saba doka. An kashe zakin ne a wajen gandun dajin kasar da ake kira Huange. Duka mutanen biyu sun musanta sun aikata laifi.
Kasr Zimbabwe tana neman a mika mata Mr. Plamer, wanda ya daina fita a bainar jama'a tun bayan da aka bayyana kashe zakin.
Namijin zakin fitacce ne a gandun dajin, kuma jami'ar Oxford ta makala masa wata na'ura shigen guru domin kiwon mu'amalarsa a gandun dajin.