Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe: An Yi Bikin Samun ‘Yanci Ba Shagulgula


Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa

Kasar Zimbabwe ta cika shekara 40 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Sai dai ba kamar sauran shekarun da suka shude ba, an yi murnar ranar ne ba tare da yin shagulgula ba.

Kasar ta kasance karkashin dokar hana zirga zirga saboda matakan da hukumomi suka dauka na yaki da cutar COVID-19.

Shugaba Emmerson Mnangagwa ya gabatar jawabinsa ga al’umar kasar ta talbijin ne a ranar Asabar daga fadar gwamti sabanin yadda aka saba a babban filin kwallon kafar kasar

“Mun yi niyyar yin wannan biki ne ta hanyar kayata shi a Lardin Bulawayo; amma kuma annobar COVID-19 da muke fuskanta ta tilasta mana zama gidajenmu.”

Ya zuwa yanzu, kasar ta Zimbabwe na da mutuum 24 da suka kamu da cutar ta coronavirus inda mutum uku suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG