Zirga zirga ta tsaya cik tsakanin kudancin Najeriya da arewa maso yammacin kasar, bayan da wasu muhimman gadoji biyu suka rufta a jahar Nija.
Ta baya bayan nan itace gadar da take Tatabu-inda masu kananan motocin dibar fasinja da suka fito daga Legas, suke msuayar fasinjoji da motoci da suka fito daga arewa maso yammacin kasar.
Daya gadar data rufta itace wacce take Bakane.
Al’amarin kamar yadda wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya aiko mana da rahoto, ya shafi harda zirga-zirgan jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.
Masu manyan motocin dakon kaya sune wannan matsala tafi shafa domin ba zasu iya zuwa inda suka dosa ba saboda wannan lamari.
Hukumomi a jahar ta Nija ta bakin kwamishinan yada Labarai, Jonathan Vatsa, yace basu da karfin yin komi kan ayyukan gyara hanyoyin domin basu da kudi, kuma hakkin gwamnatin tarayya ne. Vatsa yayi amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa na magance wannan lamari.
Yace a cikin wata daya idan gwamnatin taga dama zata magance wannan matsala.
Facebook Forum