Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZIYARAR AIKI: Buhari Ya Kasa Gane Hanyar Zuwa Gidanshi a Kaduna


Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna
Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ayyukan cigaban da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i ya yi sun sa ya kasa kai kanshi gida duk da shekarun da ya yi a matsayin mazaunin Kaduna kafin zama shugaban Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya kaddamar da ayyukan hanyoyi da gadoji da sauran ayyukan more rayuwa a yankin Kafanchan dake kudancin Kaduna da kuma wasu ayyukan a kwaryar garin Kaduna, ya ce Kaduna ta canza fasali karkashin gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i.

Da yake jawabin a wajen kaddamar da hanyoyin da gwamna El-Rufa'i ya gyara, Shugaba Buhari ya ce Kaduna gida ce a gurin shi amma yanzu da kyar ne ya gane gidan shi sabili da yadda hanyoyin suka sauya fasalin birnin Kaduna.

Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna
Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna

Tuni dai Jam'iyyar PDP mai adawa a jahar Kaduna ta yi marhaban da zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kaduna, amma ta ce ziyarar siyasa ce tsantsa kuma ta kalubalanci gwamna El-rufa'i ya wuce yankin Birnin Gwari da Giwa don jajantawa mutanen da ke fama da hare-haren 'yan-bindiga a yankin.

A hirarshi da Muryar Amurka, Alh. Ibrahim Aliyu Wusono, sakataren Jam'iyyar ta PDP a jahar Kaduna ya ce a da shugaba Muhammadu Buhari ya ce baya yawon kaddamar da ayyukan da gwamnoni ke yi domin abinda aka zabe su su yi ke nan. Ya ce kamata ya yi shugaban kasar ya je ya ziyarci wadanda suka yi fama da tashin hankalin da ake fuskanta a kasa baki daya ta matsalar tsaro amma ba ya buge a kaddamar da hanyoyi ba.

Sai dai kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta ce gajiyawa ce ta sa Jam'iyyar PDP ke korafi game da ayyukan da gwamnatin APC ta yi duk da cewa koya yana yaba yadda babban birnin jihar ya sake.

Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna
Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna

A hirarshi da Muryar Amurka, sakataren yada labaru na Jam'iyyar, Alh. Salisu Tanko Wusono ya ce, bai kamata a rufe ido a ganin ci gaban da aka samu ba, a rika neman bincika kudin da aka kashe kan aikin da kowa yana iya gani a kasa a zahirance duk da cewa akwai wadansu ayyukan da ba a kammala ba.

Ziyarar aiki ta shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jahar Kaduna dai ta kwanaki biyu ce, inda a daren nan zai halarci taron cin abuncin dare sannan gobe Juma'a kuma ya wuce Zariya don karkare kaddamar da ayyukan da gwamnatin Kaduna ta yi cikin shekaru shida da wasu watanni.

Aikin hanyoyin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Kaduna
Aikin hanyoyin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Kaduna

Saurari rahoton da Isah Lawal Ikara ya aiko a cikin sauti:

Shugaba Buhari ya kaddamar da hanyoyi a jihar Kaduna-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG