Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Buhari A Jihar Imo Ba Ta Da Amfani - PDP


Shugaba Buhari, hagu, da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo lokacin da ya kai ziyara fadar shugaban kasa a wat an Agustin 2021 (Instagram/Hope Uzodinma).
Shugaba Buhari, hagu, da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo lokacin da ya kai ziyara fadar shugaban kasa a wat an Agustin 2021 (Instagram/Hope Uzodinma).

Sai dai kwamishinan yada labarai a jihar ta Imo Declan Emelumba, ya ce akwai manyan ayyuka guda hudu da ake sa ran shugaba Buhari zai kaddamar a lokacin ziyarar.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta ce ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yrke yi a jihar ba ta da amfani.

Shugaban na Najeriya na ziyara a jihar ta Imo a ranar Alhamis kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Sai dai jam’iyyar ta PDP a jihar ta ce babu wani aiki da gwamna Hope Uzodimma ya yi da Buharin zai kaddamar.

“Jam’iyyar PDP a jihar Imo na mamakin abin da shugaba Buhari zai zo yi a jihar. Muna wannan tambaya ne saboda gwamnatin Uzodinma ba ta da wani aiki da za ta nuna, saboda haka, wannan ziyara ta shugaban kasa, ba ta da amfani.” Sakataren yada labaran jam’iyyar Ogubundu Nwadike ya ce.

Nwadike ya kara da cewa, ziyarar tamkar “izgilanci ne” ga al’umar jihar ta Imo.

Jam’iyyar ta PDP ta kara da cewa, ta yi iya bakin kokarinta wajen jawo hankalin gwamnatin Uzodinma kan ta yi wa al’uma aiki, amma abin ya ci tura.

Sai dai yayin ganawa da manema labarai a birnin Owerri a ranar Laraba, kwamishinan yada labarai Declan Emelumba, y ace al’umar jihar sun zaku da ziyarar ta Buhari kuma sun kimtsa don tarbar shi.

Emelumba ya kara da yin gargadi ga mambobin kungiyar IPOB masu fafutukar ballewa daga Najeriya, da kada su kawo cikas ga wannan ziyara.

Rahotanni sun ce kungiyar ta ba da umarnin a zauna a gida a ranar Alhamis, a wani mataki nanu na bore ga ziyarar shugaban kasar.

Kwamishinan ya ce, shugaba Buhari zai kaddamar da ayyuka guda hudu, wadanda suka hada da hanyar Ihiagwa zuwa Nekede da ta karkashin kasa a Nwoha road, Naze/Nekede/Ihiagwa sai kuma hanyar Egbeada da kuma sabon ofishin majalisar zartarwar jihar

XS
SM
MD
LG