Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Mai Martaba Sarkin Kano Zuwa Amurka


A kokarin taimakawa mutane masu karamin karfi wajen samun gidajen da zasu iya biya, mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ya gana da jami’an wata masana’anta da ake cewa IGS a takaice.

Masana’antar na sarrafa harawar shinkafa da alkama wajen gina gidaje masu karfi, kamfanin dai na nan Amurka a birnin Fort Worth dake jihar Texas, bayan da mai martaba ya gana da jami’an wannan masana’anta sai kuma aka zagaya da shi domin ganin yadda masana’antar ke aiki.

Ma’aikaciyar Sashen Hausa na Muryar Amurka Hajiya Jummai Ali, ta zanta da mai martaba sarkin Kano, kan dalilin dayasa ya dauki wannan mataki. Inda mai martaba yace “Na farko kamar yadda aka sani kafin nazo wannan matsayi, nayi aiki a babban banki Najeriya da sauran bankuna, saboda haka mun san mutane a ko’ina kuma mun kudiri niyyar cewa insha Allahu zamuyi amfani da mutanen da muka sani muga duk abin da zamu kawowa Kano cigaba, wannan shine fita ta farko akan irin wannan. Wannan aikin marigayi sarki ne, Allah yaji kansa ya gafarta masa shine yayi shawarar wani fili nasa na Darmanawa, a gina wanda ake kiransa Ado Bayero royal city, to masarauta ta zuba kudi wajen katange wannan filin, da fara saka abubuwan da ake bukata kamar hanyoyi amma masarauta bazata iya gina wannan gidajen da kudinta ba kuma bama son taci bashi.”

Mai martaba ya cigaba da cewa dalilin hakan ne yasa suka fitar da wani tsari, wanda suka sami wannan kamfanin da yake sarrafa abubuwan gina gidaje cikin arha, domin gina gidajen da basu kai gidan ciminti tsada ba kasancewar ba kowa ne keda kudi ba. Ana dai kokarin samarwa da mutane gidaje masu saukin kudi harma a samar wa da mutane hanyar da zasu samu bashi.

A yanzu haka dai masarautar ta sayo irin wadannan gidaje guda hudu da za’a je a fara gwadawa dasu a Kano, kuma suna kan hanya a yanzu haka. Masarautar na son siyar da gidajen kan kudi da bai wuce miliyan goma ba, sannan bankin Aso zasu bawa mutane bashi shekara goma zuwa shekara goma sha biyar har su sayi gidajen. A cikin wannan tsarin masarautar zatayi kokarin gina gidajen guda dari biyar a cikin shekaru biyu ko uku masu zuwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG